<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ta da ido, ka duba gonaki
 Cikin duniyan nan yanzu,
 Dukansu sun isa girbi,
 Babu ma'aikata sosai.

[V2]
 KORUS
 Ubangiji, muna roƙo,
 Lokaci 'na wucewa,
 Nuna mana wurin aiki
 Don mu kawo girbinka.

[V3]
 2) Tun da wuri sai mu tafi.
 Ko da rana kada mu ƙi.
 Ko gajiya ta zo da yamma,
 Sai mu ƙarasa aikinmu.
 Korus

[V4]
 3) Lalle za mu sha wahala
 Cikin wasu gonaki.
 Amma can a cikin Sama
 Murna, murna za mu yi.
 Korus</lyrics>
<title>Ta da Ido, Ka Duba Gonaki LW272</title>
<hymn_number>272</hymn_number>
</song>